Rahoto kai-tsaye
Ahmad Bawage da Isiyaku Muhammed
Rufewa
A nan muka kawo muku ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.
Amurka da Iran sun ce suna "tattaunawa mai amfani" kan shirin nukiliya
Asalin hoton, Getty Images
An kammala zagaye na 4 a tattaunawar makaman nukiya tsakanin Iran da Amurka a Oman, inda ɓangarorin suka amince a sake zama.
Wakilin Amurka na musamman Steve Witkoff ya ce ana yi wa ganawar kyakkyawar fata, sannan shi ma ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce tattaunawar ta yi tsauri amma mai amfani ce.
A baya dai Amurka ta dage sai Tehran ta watsar da shirinta na inganta sinadarin Uranium don kauce wa samar da makaman nukiliya.
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya ce a "shirye muku a ƙulla aminci tsakaninmu amma ba za mu yi watsi da duk wani shiri na kare kanmu ba."
Amurka ta ce tana samun fahimtar juna da China kan rikicin kasuwanci
Sakataren baitul malin Amurka Scott Bessent ya bayyana tattaunawar da ake yi tsakanin Amurka da China a matsayin "tattaunawa da ke tafiya da kyau,'
Wannan batun na zuwa ne bayan tattaunawar da ƙasashen biyu suka yi na kwana biyu a birnin Geneva da zimmar kawo ƙarshen takun-saƙar kasuwanci da ke tsakanin ƙasashen biyu da suka fi ƙarfin tattalin arziki.
Sai dai Scott bai bayyana asalin abin da suka tattauna ba, amma ya ce wasu bayanan za su fito a ranar Litinin.
Wannan ne karo na farko da ƙasashen biyu suka fara zama tun bayan da Amurka ta lafta wa China harajin sama da kashi 100, sannan ita ma China ta mayar da martani.
Ecoador ta binne sojojinta 11 da aka kashe a wajen haƙo zinare
Asalin hoton, Reuters
Ƙasar Ecuador ta yi faretin ban-girma domin binne sojojinta 11 da wasu mahara suka kashe a ranar Juma'a a wajen haƙo zinare.
Da yake jawabi a wajen bikin wanda aka yi a Quito, Ministan tsaron ƙasar Giancarlo Lofredo ya sha alwashin mayar da martani ga maharan.
A jawabansu daban-daban, kwamandojin sojin ƙasar sun ce mamatan na cikin sojoji 80 da aka tura yankin domin daƙile harkokin masu haƙo ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba.
Sun ce maharan waɗanda ake kira Border Commando daga ƙasar Columbia sun yi wa sojojin kwanton ɓauna ne, suka kashe su.
Tsagaita wuta tsakanin India da Pakistan na ƙara faɗaɗa
Tsagaita wuta tsakanin Indiya da Pakistan na ci gaba, sa'o'i bayan abokan gabar masu makaman nukuliya sun zargi juna da karya yarjejeniyar tsagaita wutar.
Wasu ƴan kasuwa a Srinagar babban birni a yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikon Indiya sun buɗe shagunansu bayan kwanaki a rufe.
An amince da yarjejeniyar ranar Asabar bayan kwashe kwana 4 ana gumurzu.
Wakilin BBC ya ce jirage marasa matauƙa da dama sun yi shawagi a saman birnin wanda aka rufe ranar Asabar.
Kusan mutum 70 aka kashe tsakanin ɓangarorin biyu.
Shugaba Trump ya yaba wa shugabannin ƙasashen game da amincewarsu da a dakata da rikicin.An gudanar da gangamin goyon bayan sojoji a yankuna da dama a Pakistan.
Ambaliya ta yi ajalin mutum 100 a DR Congo
Asalin hoton, Getty Images
Sama da mutum 100 ne suka rasu a sanadiyar ambaliyar da ta ɗaiɗaita wani ƙauye da ke gaɓar tekun Tanganyika da ke gabashihn Dimukuraɗiyyar Jamhuriyar Congo.
Wani jami'in gwamnatin ƙasar, Sammy Kalodji da aiki a gwamnatin shiyyar Fizi da ke kudancin Kivu ya ce mamakon sama ne ya janyo ambaliyar a ƙauyen Kasaba.
Kakakin gwamnatin kudancin Kivu, Didier Luganywa a wata sanarwa ya ce an yi ambaliyar ne bayan mamakon ruwan sama da aka yi a daren Alhamis, wanda ya sa gaɓar tekun Kasaba ya ɓalle.
Ambaliyar ta zo ne a daidai lokacin da ake cigaba da fafata yaƙi tsakanin dakarun gwamnatin ƙasar da dakarun M23, wanda ya yi ajalin dubban mutane.
Flick ya ci Real Madrid karo huɗu a jere a kakarsa ta farko a Barca
Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta doke Real Madrid 4-3 a wasan mako na 35 a La Liga da suka fafata ranar Lahadi a Estadi Olimpic Lluis Companys.
Barcelona ta ci ƙwallayen ta hannun Eric Garcia da Lamine Yamal da Raphinha da ya zura biyu a raga.
Ita kuwa Real Madrid, mai riƙe da La Liga na bata ta zura ƙwallayenta uku ta hannun Kylian Mbappe ta farko a bugun fenariti.
Karanta cikakken labarin a nan
Tinubu zan mara wa baya a zaɓen 2027 - Patience Jonathan
Asalin hoton, AFP
Uwargidan tsohon shugaban Najeriya Dame Patience Jonathan, ta nanata cewa ba ta da burin komawa fadar shugaban ƙasa, inda ta bayyana cewa a shirye take ta taimakawa Uwargidan shugaban ƙasa na yanzu Sanata Oluremi Tinubu wajen yaƙin zaɓen 2027.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Patience na bayyana haka ne a lokacin da take kiran sunan manyan baƙi ciki har da ƴar shugaban ƙasar, Folashade Tinubu-Ojoa wajen taron da aka karramata a matsayin jagora ta gari, wanda kamfanin Accolade Dynamics Limited ta shirya a ranar Asabar a Abuja.
Ta ce, "ita ya kamata in fara kira amma sai na bari zuw ƙarshe wato ƴar shugaban ƙasarmu wanda muka aminta da shi wato Shugaba Bola Tinubu. Iyajola ina miki godiya bisa yadda kike ƙarfafa gwiwar mata. Muna tare da ke a wannan aikin kuma za mu mara miki baya.
"Ina da yawan magana, idan ba na son abu ana ganewa, amma idan ina tare da abu, zan iya mutuwa a kansa. Kowa da lokacinsa a mulki, kuma idan lokacin mutum ne, ina goya masa baya ne."
Ta ƙara da cewa a lokacin da suke mulki, Uwargidan shugaban ƙasa Oluremi Tinubu ta goya mata baya. "Ina da hankali, don haka dole ne in mayar da biki. Na faɗa mata cewa zan taya ta yaƙin zaɓe, ba zan juya mata baya ba. Ni ba na sha'awar komawa fadar shugaban."
Burkina Faso ta buƙaci tallafin Rasha wajen horar da matasan ƙasarta ɓangaren kimiyya da fasaha
Asalin hoton, AFP
Kafar watsa labaran RTB mallakin ƙasar Burkina Faso ta ruwaito cewa shugaban mulkin sojin ƙasar, Ibrahim Traore ya buƙaci Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ƙara ƙaimi wajen horar da matasan ƙasarsa a ɓangaren kimiyya da sauran ɓangarorin ilimi.
Kafar ta ruwaito cewa Traore ya bayyana haka ne a ziyarar da ya kai Moscow a matsayin "baƙo na musamman" a bikin cika shekara 80 da ƙasar ta yi na samun galaba a kan sojojin Nazi na Jamus.
Traore ya nanata buƙatar da suke da ita ga Rasha na horar da matasan ƙasar a ɓangaren kimiyyar, "domin mu samu nasarar ciyar da ƙasarmu gaba."
Haka kuma shugabannin ƙasashen biyu sun tattauna ƙarin goyon bayan soji ga Burkina Faso.
Fafaroma Leo ya yi kiran 'samar da zaman lafiya mai ɗorewa' a duniya
Asalin hoton, Reuters
Fafaroma Leo na 14 ya yi kiran "dakatar da yaƙi" a wani sako ga shugabannin duniya a jawabin ranar Lahadi na farko da ya gabatar a fadar Vatican.
Da yake magana kan rikice-rikice, sabon Fafaroman ya yi kiran "samar da zaman lafiya mai ɗorewa" a yaƙin Ukraine da tsagaita wuta a Gaza, ya kuma yi farin ciki da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma ranar Asabar tsakanin Indiya da Pakistan.
Ya ce "ba ya jin daɗin" abubuwan da ke faruwa a Gaza, inda ya yi fatan "zaman lafiya mai dorewa" tsakanin Indiya da Pakistan, har ma da Ukraine.
A zaɓi Fafaroma Leo ne a matsayin jagoran cocin Katolika ranar Alhamis, bayan zaɓe da aka gudanar a birnin Vatican da kuma mutuwar wanda ya gada Fafaroma Francis.
A ranar Asabar, ya kai ziyara wurin bauta a wajen birnin Rome da kuma yi wa kabarin Fafaroma Francis addu'a wanda aka binne a cocin St Maria Maggiore.
Za a yi bikin naɗin Fafaroma Leo ne a wani taron addu'a a dandalinSt Peter's ranar 18 ga watan Mayu.
Ƴan wasan Sevilla sun kwana a filin atisaye kan yunkurin far musu daga magoya baya
Asalin hoton, Getty Images
Ƴan wasan ƙungiyar kwallon kafa ta Sevilla sun shafe dare a filin atisaye a yammacin ranar Asabar bayan da suka gamu da fushin magoya bayansu.
Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta yi Alla-wadai da lamarin har ma da waɗanda suka yi yunkurin "yin ɓarnar" kayayyaki a filin su na atisaye, bayan doke su da ci 3-2 da Celta Vigo ta yi.
Hotunan bidiyo da aka yaɗa a kafofin sada zumunta sun nuna wasu magoya baya na yin sowa a wajen filin da kunna abubuwan tartsatsin wuta - yayin da wasu kuma aka nuna ɓata kofar shiga filin atisayen.
Lamarin ya tilastawa ƴan wasa da kuma ma'aikatan ƙungiyar kwana a cikin filin bayan dawowa daga buga wasa da Celta Vigo.
Sevilla ta ƙara da cewa "za ta yi ƙoƙarin yin bincike don gano waɗanda ke da hannu a lamarin, kuma ba za ta sassauta ba idan har ta gano magoya bayanta na ciki.
Sevilla na mataki na 16 a teburin La Liga, bayan rashin nasara a hannu Celta Vigo - inda ya rage mata wasanni uku.
Duniya na jiran ganin an tsagaita wuta a yaƙin Ukraine - Firaministan Poland
Asalin hoton, EPA
Firaiministan Poland Donald Tusk ya mayar da martani kan buƙatar tayin tattaunawa kai-tsaye da Ukraine da Putin ya yi.
Tusk yana cikin shugabannin Turai da suka kai ziyara Kyiv a ranar Asabar don ganawa da shugaba Zelensky.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Firaministan na Poland ya sake nanata cewa suna son Rasha ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon kwanaki 30, farawa daga gobe Litinin.
"A martani ga buƙatar mu, Rasha ta nemi zama don tattaunawa ranar Alhamis 15 ga watan Mayu. Sai dai, duniya tana jiran ganin mataki kan yarjejeniyar tsagaita wuta ta nan take kuma mara shinge.
"A shirye Ukraine take. Babu wanda za a sake gallazawa," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
NDLEA ta kama wata mata ɗauke da hoda iblis a filin jirgin sama a Fatakwal
Asalin hoton, NDLEA
Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA sun ce sun kama wata mata da ta yi yunkurin fita da hodar iblis zuwa ƙasar Iran.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya fitar, ya ce an kama matar ce a filin jirgin sama a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas - inda ta saka hodar iblis ɗin a cikin al'aurarta da cikinta da kuma a wata jaka.
Babafemi ya ce matar mai suna Ihensekhien Miracle Obehi, wadda ta saka hijabi domin ƙoƙarin tsallake binciken jami'an tsaro, an cafke ta ne a Lahadin da ya gabata lokacin da take yunkurin shiga jirgin Qatar Airline zuwa Doha, kafin ta wuce Iran.
Ya ƙara da cewa yayin bincike, an gano matar ta saka ƙunshin hodar iblis har uku cikin al'aurarta, sannan ta saka wani a jakarta sai kuma ta haɗiye ƙwayoyi 67 a cikinta.
Sakamakon haka, an tilasta ta yin aman ƙwayoyin da kuma wanda ta saka a cikinta da al'aurarta.
Obehi ta yi iƙirarin cewa an saka ta ta haɗiye ƙwayoyin hobar iblis 70, sai dai bayan haɗiye 67 ta ƙasa haɗiye sauran - inda ta yanke shawarar saka su a al'aurarta, a cewar Babafemi.
An sake kama fasto ɗan Najeriya da aka wanke kan zargin fyaɗe
Asalin hoton, Getty Images
An sake kama wani fasto ɗan Najeriya da aka wanke kan zargin aikata fyaɗe, a cewar ƴansandan Afirka ta Kudu.
Ƴansandan sun ce an kama faston ne a ranar Asabar, sai dai a yanzu ana zarginsa da laifuka da suka shafi shige da fice.
An sake Timothy Omotoso ne a watan da ya gabata, bayan zama a gidan yari na tsawon shekaru tara yana jiran shari'a kan laifin fyaɗe da kuma cin zarafin lalata da wasu ƴan mata daga cocinsa.
Wanke shi da aka yi - ya janyo fushi a faɗin Afirka ta Kudu.
Duk da cewa maganganun faston ba lallai su zama gaskiya ba, masu gabatar da ƙara sun yi kuskure wajen gudanar da shari’ar da ake yi masa, a cewar alkalin da ya jagoranci shari'ar.
Hukumomin shige da fice da kuma ƴansanda sun kama Omotoso ne a garin East London a safiyar Asabar, jim kaɗan bayan kammala ibada a cocinsa, kamar yadda kwamishinan ƴansandan lardin ya faɗa wa manema labarai.
"Zai fuskanci tuhuma da ta shafi saɓa wa dokar shige da fice, kuma zai gurfana gaban kotu ranar Litinin," in ji ƴansanda.
El Clasico: Wa zai haska Yamal ko Mbappe?
Asalin hoton, Getty Images
A yau Lahadi ne Barcelona za ta ɓarje gumi da Real Madrid a wasan El Clasico da za su fafata a filin wasa na Olympic.
Gabanin wasan dai, ana ta magana kan rawar da Lamine Yamal ke takawa a kakar bana - musamman a Champions League da suka kai daf da karshe, inda Inter Milan ta fitar da Barcelona.
Matashin ɗan wasan mai shekara 17 ya bayar da ƙwallo 21 aka zura a raga a dukkan fafatawa, sannan ya ci 14.
Cikin karawar ta EL Clasico a bana, Yamal ya ci ƙwallo biyu ya bayar da biyu aka zura a raga kawo yanzu.
Kylian Mbappe, wanda lokacin da yake da shekara 17, shi ma an yi ta batunsa, yanzu yana taka rawar gani a kakar farko a Real Madrid.
Ƙyaftin ɗin tawagar Faransa, mai shekara 26 ya ci ƙwallo 35 a dukkan fafatawa a Real Madrid a kakar nan.
A jerin masu cin ƙwallaye a La Liga a kakar nan yana mataki na biyu da 24 a raga, bayan da Robert Lewandowski na Barcelona ke matakin farko da kwallo 25.
Abu ne mai kyau yunkurin Rasha na son kawo karshen yaƙi - Zelensky
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce yunkurin kawo karshen yaƙi da Rasha ta nuna "abu ne mai kyau", bayan da Rasha ta yi tayin tattaunawa kai-tsaye ranar Alhamis mai zuwa.
Kalamansa na zuwa ne bayan da shugaban Rasha Vladimiri Putin ya gayyaci Ukraine ta shiga "tattaunawa mai ma'ana".
Sai dai shugaban na Ukraine ya ce: "Muna son Rasha ta tabbatar da tsagaita wuta - kuma mai ɗorewa - fara wa daga gobe Litinin 12 ga watan Mayu, kuma Ukraine a shirye take don a tattauna."
An buƙaci Rasha ta tsagaita wuta na tsawon kwanaki 30 fara wa daga gobe Litinin, bayan da shugabannin Turai suka jagoranci wani zama a Kyiv ranar Asabar.
An ceto ƴar shekara biyu da aka sayar kan 100,000 a Abuja
Asalin hoton, NAPTIP/X
Hukumar da ke yaƙi da fataucin mutane a Najeriya, NAPTIP ta ce ta ceto wata yarinya ƴar shekara biyu da aka yi safararta zuwa jihar Abia daga Abuja.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Juma'a, ta ce hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ne suka kama wanda ya yi safararta, inda ake zargin ya sayar da da ita kan naira 100,000.
"Mun samu nasarar ceto Chiamaka Favor, bayan safararta daga Abuja zuwa Aba a watan Febrairun 2025.
"Ana zargin wanda ya yi safararta ya yi aiki da wasu ƙungiyoyin safarar mutane uku a Abuja - sannan ya sayar da ita ga wani kan naira 100,000. Muna ci gaba da bincike," in ji NAPTIP.
Hukumar ta kuma yi kira ga iyayen yarinyar ko ƴan uwanta da su hanzarta su tuntuɓe ta domin karɓar ƴarsu.
Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Shin Fafaroma yana aure?
Asalin hoton, Getty Images
A baya, an taɓa yin Fafaroma da ya yi aure, kamar Saint Peter da ake ɗauka a matsayin Fafaroma na farko yana da mata, amma a zamanin yanzu, zai yi wuya a zaɓi wande ke da aure a matsayin Fafaroma.
Tarihin Fafaroma na farko yana da rikitarwa kuma yana janyo muhawara a tsakanin masana tarihi.
Ba a da tabbacin adadin Fafaroma da suka kasance masu aure kafin su zama shugabannin cocin Katolika kamar Saint Peter.
Karanta cikakken labarin a nan...
Atiku ya soki EFCC kan tsare Hon Gudaji Kazaure
Asalin hoton, Atiku Abubakar/X
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya soki hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC kan tsare tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya, Hon Muhammad Gudaji Kazaure.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya kwatanta kama Kazaure da kuma tsare shi a matsayin saɓa wa doka.
"EFCC ta sake aikata abin da ta saba na take doka, ta hanyar kamawa da kuma tsare ƴan ƙasa da ba su aikata laifin komai ba," in ji Atiku.
Ya yi misali da labarin fitattcen ɗan gwagwarmayar nan Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da Verydarkman wanda EFCC ta kama amma ta sake shi bayan matsin lamba daga wajen ƴan ƙasar.
"Yanzu kuma hukumar ta koma kan Gudaji Kazaure. Sun kama shi ba tare yin wani bayani na laifi da suke tuhumarsa da aikatawa ba.
"An ɗauke shi daga Kano zuwa Abuja, kuma har yanzu babu wani bayani da EFCC ta yi wa iyalansa da kuma ƴan Najeriya," a cewar Atiku.
Ya ce ko da akwai abin da mutum ya aikata - to ya kamata a bi hanyar shari'a wajen gurfanar da shi.
"Hakkin hukumar ne ta fito ta yi wa jama'a bayani kan abin da ya sa ta kama Kazaure, kuma bai kamata su riƙa tsare mutane da sunan yin bincike ba.
"Ƴan Najeriya sun zuba ido suna kallo. Kuma tarihi ba zai manta ba," in ji Wazirin na Adamawa.
Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Atiku ya soki Tinubu kan ƙoƙarin tauye haƙƙin ƙungiyoyin farar hula
An fara samun kwanciyar hankali a Indiya da Pakistan bayan tsagaita wuta
An fara samun kwanciyar hankali jim kaɗan bayan tsagaita wuta tsakanin India da Pakistan, bayan shafe kwanaki huɗu suna faɗa da juna.
Sai dai wakilin BBC ya ce bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wutar, anji ƙarar ababen fashewa na mintuna a yankin Kashmir.
Babban jami'in diflomasiyyar India Vikram Misri, ya shaida wa manema labarai cewa Pakistan ta karya yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma, yayin da ita ma Pakistan ɗin ta zargi Indiya da aikata makamancin haka.
Rikici tsakanin Pakistan da Indiya ya ɗau sabon salo